Koma ka ga abin da ke ciki

Koma secondary menu

Shaidun Jehobah

Hausa

Iyayena Ba Su Yarda da Ni Ba

Iyayena Ba Su Yarda da Ni Ba

Abin da za ka iya yi

Bincika: Abubuwan da kake yi suna sa iyayenka su ki yarda da kai ne?

Alal misali, manzo Bulus ya rubuto: “Muna so mu yi tasarrufin kirki cikin dukan abu.” (Ibraniyawa 13:18) Ka tambayi kanka, ‘Wane hali aka san ni da shi a batun gaya wa iyayena gaskiya game da wuraren da nake zuwa da kuma abubuwan da nake yi?’

Ka zabi suna guda a kasa don samun labari na gaske.

 Lori  Beverly

 Lori

Ina aika wa wani yaro sakon imel a asirce. Da iyayena suka sani, sai suka ce na daina. Na ce zan daina amma ban daina ba. Na yi ta haka har shekara guda. Sa’ad da na aika wa yaron sakon imel kuma iyayena suka gano, sai na ba su hakuri na ce ba zan kara ba amma sai in ci gaba da yi. Har turi ya kai jikin bango kuma iyayena daina yarda da ni game da kome!

Me ka ke ganin ya sa iyayen Lori suka daina yarda da ita kuma?

Da kai ne iyayen Lori, me za ka yi, kuma don me?

Da mene ne ya kamata Lori ta yi lokacin da iyayenta suka soma yi mata magana game da batun?

 Beverly

“Iyayena ba su yarda da ni ba sam game da zancen samari, amma yanzu na ga dalilin da ya sa. Ina kwarkwasa da wasunsu da suka girme ni da shekara biyu. Ina kuma magana sosai da su a kan waya, kuma a duk lokacin da muka hadu da su a wani wurin taro nakan yi tadi da su kadai in kyale sauran mutane. Iyayena suka kwace waya ta har tsawon wata guda, kuma sun hana ni zuwan duk wuraren da sun san samarin nan suke kasancewa.

Dā kai iyayen Beverly ne, dā me za ka yi, kuma don me?

Kana ganin cewa abin da iyayen Beverly suka yi bai dace ba ne? Idan haka ne, me ya sa?

Me ya kamata Beverly ta yi don ta sa iyayenta su soma yarda da ita?

Sake Samun A Yarda da Kai

Abin da za ka iya yi

Zama matashin da aka yarda da shi yana kama ne da hawa tsanin bene, daki-daki, har ya girma

Na farko, ka san abubuwan da ya sa ba a yarda da kai ba.

 • Bin dokar lokacin koma gida

 • Cika alkawuran da na yi

 • Kasancewa a kan lokaci

 • Yadda nake bi da kudi

 • Gama aikina na gida

 • Ka farka ka tashi ba sai an tilasta maka ba

 • Adana dakina da kyau

 • Fadin gaskiya

 • Yin amfani da waya ko kwamfuta a hanyar da ta dace

 • Yarda da laifina da kuma neman gafara

 • Wasu

Na biyu, tsai da shawara. Ka kafa makasudi don ka sa a yarda da kai a wuraren da ka ambata din nan. Ka bi gargadin Littafi Mai Tsarki: ‘Ka tube, ... irin zamanka na dā, tsohon mutum.’ (Afisawa 4:22) A kwana a tashi, kowa har da iyayenka za su ga ci gabanka.—1 Timotawus 4:15.

Na uku, ka gaya wa iyayenka abin da ka tsai da shawara a kai. Maimakon kana gunagunin cewa ba sa yarda da kai, cikin ladabi ka tambaye su abin da kake bukatar yi don su yarda da kai.

Abin lura: Kada ka yi tsammanin cewa iyayenka za su yarda da kai nan da nan. Babu shakka za su so su tabbatar da cewa ka cika alkawuranka. Ka yi amfani da wannan zarafin ka nuna cewa za a iya yarda da kai. A kwana a tashi, iyayenka za su soma yarda da kai kuma su ba ka ’yanci. Abin da ya faru da Beverly ke nan, da aka ambata dazu. Ta ce “ya fi sauki a daina yarda da mutum fiye da a amince da shi,” ta dada, “yanzu ana yarda da ni, kuma ina jin dadin haka!”

Gaskiyar al’amarin ita ce: Idan ka kasance da gaskiya, hakan zai sa a fi yarda da kai.