Koma ka ga abin da ke ciki

TAMBAYOYIN MATASA

Halitta ko Ra’ayin Bayyanau?​—Sashe na 2: Abin da Ya Sa Ya Kamata Ka Saka Ayar Tambaya a kan Koyarwar Ra’ayin Bayyanau

Halitta ko Ra’ayin Bayyanau?​—Sashe na 2: Abin da Ya Sa Ya Kamata Ka Saka Ayar Tambaya a kan Koyarwar Ra’ayin Bayyanau

Alex ya rikice. Ya yi imani da Allah kuma ya yi imani cewa Allah ne ya halicci kome. Amma yau malaminsa mai koyar da ilimin halittu ya ce ra’ayin bayyanau gaskiya ne domin kwararren binciken da ’yan kimiyya suka yi ya nuna hakan. Alex ba ya so a dauka shi wawa ne domin a cewarsa, ‘Idan masanan kimiyya sun tabbatar da cewa ra’ayin bayyanau gaskiya ne, na isa in musanta abin da suka ce?’

 Hakan ya taba faruwa da kai? Mai yiwuwa a duk rayuwarka ka yi imani da abin da Littafi Mai Tsarki ya fada cewa: “Allah ya halicci sama da kasa.” (Farawa 1:1) Amma, a kwanan nan mutane suna kokari su shawo kanka don ka gaskata cewa Allah bai halicci kome ba amma abubuwa sun bayyana haka kawai. Ya kamata ka yarda da su ne? Me ya sa ya kamata ka yi shakkar ra’ayin bayyanau?

 Dalilai biyu da za su sa ka yi shakkar ra’ayin bayyanau

 1.   Bakin masanan kimiyya bai zo daya a kan batun ra’ayin bayyanau ba. Duk da shekaru da masanan kimiyya suka yi suna bincike, har yanzu ba su taba ba da bayanin da bakinsu ya zo daya a kai ba.

   Ka yi tunani a kai: Idan bakin ’yan kimiyya bai zo daya a kan batun ra’ayin bayyanau ba, kuma su ne kwararrun masana, to, ai ba laifi ba ne idan ka yi shakkar wannan koyarwar.​—Zabura 10:4.

 2.   Yana da muhimmanci ka tabbata abin da ka yi imani da shi. Wani yaro mai suna Zachary ya ce: “Idan rayuwa ta soma haka kawai kwastam, to rayuwarmu da kuma abubuwan da ke sararin samaniya duk ba su da ma’ana ke nan.” Gaskiyar Zachary ne domin, idan abubuwa sun bayyana haka kwatsam, rayuwa ba za ta kasance da wata ma’ana na dindindin ba. (1 Korintiyawa 15:32) Akasin haka, idan Allah ne ya halicci kome hakan na nufin cewa za mu iya sanin manufar rayuwa da kuma yadda rayuwa za ta kasance a nan gaba.​—Irmiya 29:11.

   Ka yi tunani a kai: Ta yaya sanin gaskiya game da ra’ayin bayyanau da halitta zai canja rayuwarka?—Ibraniyawa 11:1.

 Tambayoyi da ya kamata ka yi la’akari da su

 DA’AWA: ‘Kome a sararin samaniya ya fito ne haka kwatsam.’

 •   Mene ne ko kuma wane ne ya sa abubuwa suka fito haka kwatsam?

 •   Wanne ne ya fi dacewa—a ce abubuwa sun fito haka kwatsam ko kuma wani ne ya halicci abubuwa?

 DA’AWA: ‘Mutane sun fito ne daga dabbobi.’

 •   Idan ’yan Adam sun fito daga dabbobi, alal misali gwaggo—me ya sa iyawar dan Adam da na gwaggo bai zo kusa ba ko kadan? *

 •   Me ya sa halittu, kome kankantansu, suna da wuyar fahimta? *

 DA’AWA: ‘An tabbatar da ra’ayin bayyanau.’

 •   Wanda yake ba da wannan hujjar ya taba bincika batun da kansa?

 •   Hakika, ba yawancin mutane suna imani da ra’ayin bayyanau ne kawai domin an ce musu duka masu basira suna imani da shi ba?

^ Wasu sun ce ’yan Adam sun fi gwaggo basira domin suna da babban kwakwalwa. Amma don ka san dalilin da ya sa wannan hujjar ba ta taka kara ya karye ba, ka duba kasidar nan The Origin of Life—Five Questions Worth Asking, shafi na 28.

^ Ka duba kasidar nan The Origin of Life—Five Questions Worth Asking, shafuffuka na 8-12.