Koma ka ga abin da ke ciki

TAMBAYOYIN MATASA

Halitta ko Ra’ayin Bayyanau?​—Sashe na 1: Me Ya Sa Za Ka Yi Imani da Allah?

Halitta ko Ra’ayin Bayyanau?​—Sashe na 1: Me Ya Sa Za Ka Yi Imani da Allah?

 Halitta ko Ra’ayin Bayyanau?

Ka gaskata cewa Allah ne ya halicci dukan abubuwa? Idan haka ne, ba kai ne kadai ba; matasa da yawa (da manya) ma sun gaskata da haka. Amma wasu sun ce “Allah” bai halicci rai da kuma sararin samaniya ba, amma sun fito ne kawai.

Ka sani kuwa? Mutane da suka yi imani da ra’ayin bayyanau da kuma wadanda suka yi imani da halitta suna saurin fadin imaninsu ba tare da sanin ainihin dalilin da ya sa suka yi imani da batun ba.

 • Wasu mutane sun yi imani da halitta ne kawai don abin da aka koya musu a coci.

 • Yawancin mutane kuma sun yi imani da ra’ayin bayyanau don abin da aka koya musu a makaranta.

Jerin talifofin nan za su taimaka maka ka inganta kuma ka bayyana imaninka game halitta. Da farko, kana bukatar ka yi wa kanka wata tambaya mai muhimmanci:

 Me ya sa na yi imani da Allah?

Me ya sa wannan tambayar take da muhimmanci? Domin Littafi Mai Tsarki ya karfafa ka ka yi amfani da hankalinka. (Romawa 12:⁠1) Hakan na nufin cewa ya kamata ka kasance da kwararren dalilai da suka sa ka yi imani da Allah, ba don

 • yadda kake ji ba (A ganina, dole ne akwai wanda ya fi girma)

 • ra’ayin wasu ba (Ina zama a yankin da mutane suna zuwa coci sosai)

 • matsi (Iyayena sun rene ni yadda dole na yi imani da Allah)

  Maimako, ka tabbatar wa kanka cewa Allah ya wanzu kuma ka kasance da kwararren dalilai don imaninka.

Me ya sa ka tabbata cewa Allah ya wanzu? Shafin rubutun nan mai jigo “Me Ya Sa Na Yi Imani da Allah?” zai inganta imaninka. Bincika yadda wasu matasa suka amsa wannan tambayar ma zai taimaka maka.

Teresa ta ce: “A duk lokacin da nake cikin aji kuma malaminmu yana bayyana mana yadda jikinmu ke yin aiki, hakan na sa in tabbatar wa kaina cewa Allah ya wanzu. Duka gabbobin jikinmu suna da aikinsu, har da kananan gabbobin jikinmu, kuma a yawancin lokaci, wadannan gabbobin jikinmu suna aikinsu ba tare da saninmu ba. Hakika, jikin ’yan Adam abin ban mamaki ne!”

Richard ya ce: “Idan na ga gini mai tsawo, da jirgin ruwa mai girma da kuma mota, ina yi wa kai na tambaya, ‘waye ne ya kera wadannan?’ Babu shakka, wadanda suka kera mota suna da basira sosai. Dole ne kananan kayyakin motar su yi aiki da kyau kafin motar ta yi aiki baki daya. Idan wani ne ya kera mota, to lallai ne cewa akwai wanda ya halicci ’yan Adam.”

Karen ta ce: “Idan ka yi la’akari da yawan shekaru da yake daukan masu ilimi suna neman fahimin wani karamin sashe cikin sararin halitta, wauta ne yin tunanin cewa babu wani mai basira da ya halicci wannan sararin!”

Anthony ya ce: “Yayin da nake dada ci gaba a nazarin kimiyya, hakan na sa ni ganin cewa babu wata shaida da ta tabbatar da ra’ayin bayyanau. Alal misali, na yi la’akari da yadda dukan halittu da kuma ’yan Adam suke da tsari sosai, da kuma yadda muke bukatar mu san ko wane ne ne mu, da wurin da muka fito da kuma wurin da za mu koma. Masu koyar da ra’ayin bayyanau suna kokarin bayyana dukan abubuwan nan a hanyar da ta shafi dabbobi, amma ba su taba iya ba da bayani a kan dalilin da ya sa ’yan Adam sun bambanta ba. A ganina, ya fi ‘wuya’ a gaskata da ra’ayin bayyanau fiye da gaskata cewa akwai Mahalicci.”

 Yadda zan bayyana imanina

Idan abokan ajinka suna maka ba’a don ka yi imani da abin da ba ka gani ba fa? Idan suka ce ai kimiyya ta “tabbatar” da ra’ayin bayyanau kuma fa?

Da farko, ka kasance da gaba gadi cewa abin da ka yi imani da shi gaskiya ne. Kada ka ji tsoro ko kuma ka ji kunya. (Romawa 1:​16) Ban da haka ma, ka tuna cewa:

 1. Ba kai ne kadai ba; akwai mutane da yawa da suka gaskata da Allah. Wadannan mutanen sun kunshe mutane masu basira sosai da kuma masu sana’a. Alal misali, da akwai ’yan kimiyya da suka gaskata da Allah.

 2. Wasu lokatai, idan mutane suka ce ba su gaskata da Allah ba, watakila suna nufi ne cewa ba su fahimci ko wane ne Allah ba. Maimakon su ba da tabbacin da ya goyi bayan ra’ayinsu, suna tambayoyi irin su, “Idan Allah ya wanzu, me ya sa ya kyale shan wahala?” Sun juye batu mai muhimmanci zuwa yadda suke tunani kawai.

 3. ’Yan Adam suna da bukatar kulla dangantaka da Allah. (Matta 5:⁠3, NW) Wannan ya kunshe bukatar yin imani da Allah. Saboda haka, idan wani ya ce Allah bai wanzu ba, mutumin ne ke da hakkin ba da bayanin abin da ya sa ya fadi haka, ba kai ba ne.​—Romawa 1:​18-​20.

 4. Yin imani da Allah ba wauta ba ne. Tabbaci ya nuna cewa akwai wanda ya halicci rai. Babu wani tabbaci da ya nuna cewa wani abu marar rai ne ya juya ya zama abu mai rai.

  To, me za ka ce idan wani ya yi maka tambaya game da imaninka da Allah? Ka lura da wadannan yanayoyin.

Idan wani ya ce: “Jahilai ne kawai suke gaskata da Allah.”

Za ka iya cewa: “Ashe kai ma ka yarda da wannan ra’ayin? Ni ban yarda da shi ba. A wani bincike da aka yi da gwanayen ’yan kimiyya sama da 1,600 daga jami’o’i dabam-dabam suke ciki, an sami kashi uku cikinsu sun gaskata cewa Allah ya wanzu wasu kuma ba su gaskata da haka ba. * Za ka ce wadannan gwanaye jahilai ne domin sun gaskata cewa akwai Allah?”

Idan wani ya ce: “Idan da gaske ne cewa Allah ya wanzu, me ya sa wahala ta yi yawa a duniya?”

Za ka iya ce: “Watakila kana nufin ba ka fahimci yadda Allah yake yin abubuwa ba ko kuma ka dauka cewa ba ya daukan mataki a kan wahalar da muke sha. Ko ba haka ba? [Ka bari ya ba da amsa.] Na riga na samu amsa mai gamsarwa game da dalilin da ya sa wahala ta yi yawa a duniya. Amma mutum na bukatar ya bincika wasu koyarwar Littafi Mai Tsarki kafin ya fahimce amsar tambayar. Shin za ka so ka samu karin bayani?”

Talifin da zai biyo wannan zai tattauna dalilin da ya sa masu koyar da ra’ayin bayyanau ba su iya ba da bayani mai gamsarwa game da wanzuwarmu ba.

^ sakin layi na 32 Daga: Social Science Research Council, “Religion and Spirituality Among University Scientists,” na Elaine Howard Ecklund, 5 ga Fabrairu 2007.