Koma ka ga abin da ke ciki

TAMBAYOYIN MATASA

Yana da Muhimmanci a Kafa Dokoki a Gida?

Yana da Muhimmanci a Kafa Dokoki a Gida?

 Kana ganin dokokin da iyayenka suka kafa suna takura maka ne? Wannan talifin da kuma shafin rubutunsa zai taimaka maka ka san yadda za ka tattauna batun da iyayenka.

 Yadda ya kamata ka dauki dokokin

 Karya: Idan na bar gida, ba wanda zai kara kafa min dokoki.

 Gaskiya: Ko da mutum ya bar gida, ba zai iya guje wa dokoki ba. Domin dole ne ya bi dokokin shugaban wurin aikinsa ko na maigidan da yake zaune ko kuma na gwamnati. Wata ’yar shekara 19 mai suna Danielle ta ce: “A ganina, duk wani matashin da ba ya son ya bi dokokin iyayensa zai sha mamaki idan ya soma zaman kansa.”

 Littafi Mai Tsarki ya ce: Ku ‘yi biyayya ga mahukunta da masu iko.’ (Titus 3:1) Kuma idan bin dokokin iyayenmu yana mana sauki yanzu, hakan zai taimaka mana mu bi dokoki a waje bayan mun girma.

 Abin da za ka iya yi: Ka yi tunani a kan amfanin dokoki. Wani matashi mai suna Jeremy ya ce: “Dokokin da iyayena suka kafa min sun taimaka min in rika yin abubuwa masu muhimmanci da lokacina, hakan ya sa na rage kallon TV da buga wasan bidiyo kuma na sami abokan kirki.”

 Yadda ya kamata ka daidaita batun

 Idan kana ganin kamar dokar da aka ba ka tana takura maka fa? Alal misali, wata matashiya mai suna Tamara ta ce: “Iyayena sun bar ni in tafi har kasar waje, amma yanzu da na dawo gida, ba sa bari na in tafi nan da can ko da wuri mai nisan minti 20 ne kawai!”

 A ce kai ne a irin wannan yanayin, shin, zai dace ka tattauna batun da iyayenka? Zai dace! Sirrin shi ne, ka san yadda ya kamata ka yi musu magana da kuma lokacin da ya dace ka yi hakan.

 Lokaci da ya kamata ka yi magana. “Wata matashiya mai suna Amanda ta ce: “Iyayenka za su iya amincewa da ra’ayinka idan ka riga ka dade kana yin abubuwa da suka dace.”

 Wata kuma mai suna Daria ta ce abin da Amanda ta fada gaskiya ne. Shi ya sa ta ce: “Sai da mahaifiyata ta ga cewa ina mata biyayya sosai kafin ta soma amincewa da ra’ayina.” Yana da kyau mu san cewa wajibi ne mu rika yi wa iyayenmu biyayya sosai kafin su yarda da ra’ayinmu, ba dole za mu sa su su amince da shi ba.

Zama a gidan da ba a bin dokoki, yana kama da saukowa a filin jirgin sama da ba a bin dokokin zirga-zirgar jiragen sama

 Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ka kiyaye umurnin ubanka, dokar uwarka kuma kada ka yashe ta.” (Misalai 6:20) Sai ka dade kana yi wa iyayenka biyayya sosai kafin su amince da ra’ayinka ko su yarda ku tattauna batun dokoki da su.

 Ta yaya za ka yin hakan. Wani matashi mai suna Steven ya ce: “Sa’ad da kake tattaunawa da iyayenka, zai fi dacewa ka daraja su kuma ka yi musu magana cikin natsuwa maimakon ka rika gardama da su ko kuma ihu.

 Daria, wadda aka yi maganarta dazu, ta yarda da hakan kuma ta ce: “Yin gardama da mahaifiyata ba ya canja kome, sai dai ya sa ta ta kara wasu dokokin.”

 Littafi Mai Tsarki ya ce: “Wawa yakan furta dukan fushinsa; amma mai hikima yakan danne shi ya kwabe shi.” (Misalai 29:11) Babu shakka, kasancewa da hakuri zai taimaka maka ba a gida kawai ba, amma har a makaranta da wurin aiki, da ma duk inda kake.

 Abin da za ka iya yi: Ka yi tunani kafin ka yi magana. Idan ka yi wa iyayenka magana da fushi, za ka iya bata suna mai kyau da kake da shi a gabansu. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Mai jinkirin fushi yana da fahimi mai girma.”—Misalai 14:29.

 Taimako: Ka yi amfani da shafin rubutu na wannan talifin wajen yin tunani sosai game da dokokin da iyayenka suka kafa, kuma ku tattauna su tare.