Koma ka ga abin da ke ciki

Shaidun Jehobah

Ka Zabi Yare Hausa

TAMBAYOYIN MATASA

Yaya Zan Daina Yin Jiki?

Yaya Zan Daina Yin Jiki?

Littafi Mai Tsarki ya yi magana a kan kasance “mai-kamewa.” (1 Timotawus 3:2) Hakan ma ya shafi yadda muke cin abinci. Tun da haka ne, za mu iya bin shawarwarin da ke gaba.

Ka san lokacin da ka koshi. Wata ’yar shekara 19 mai suna Julia, ta ce: “A dā na cika damuwa da yawan abincin da nake ci, amma yanzu, nakan daina cin abinci idan na koshi.

Ka guji abincin da zai sa ka rashin lafiya. Wani dan shekara 21 mai suna Peter ya ce: “Sa’ad da na daina shan kayan zaki, na rage nauyin kilo 5 a cikin wata daya!

Ka guje wa mummunar halin cin abinci. Wata ’yar shekara 19 mai suna Erin ta ce: “Idan na gama abincin da ke kwanona, ba na kara wani.

Abin da zai sa ka yi nasara: Kada ka ki cin abinci idan lokaci ya yi! Domin haka zai sa ka yunwa sosai kuma ya sa ka cin abinci mai yawa daga baya.

Amma, ba dukan mutanen da suke gani cewa suna da jiki sosai suke da wannan matsalar ba. Ra’ayinsu game da siffarsu ne ba daidai ba. Amma, idan kana bukatar rage nauyi da gaske fa? Ka karanta abin da Catherine ta ce ya taimaka mata.

“A dā ni matashiya ce mai jiki sosai, kuma ban ji dadin haka ba. Na yi bakin ciki sosai har na ji kamar rashin lafiya nake yi!

“Duk lokacin da na yi kokarin rage nauyin jikina ta wajen rage cin abinci, nakan sake yin jiki daga baya. Sa’ad da na kai shekara 15, sai na ce wannan abin ya isa haka. Ina son na rage kiba yadda zan iya bi da shi a nan gaba.

“Na sayi wani littafi a kan ka’idodin cin abinci da kuma motsa jiki, na karanta littafin kuma na yi amfani ka’idodin a rayuwata. Na kudura anniya cewa idan na kasa bin wannan tsarin ko kuma na yi sanyin gwiwa a wani lokaci, ba zan daina ba.

“Ka san abin da ya faru? Na cim ma burina! A cikin shekara daya, na rage nauyin kilo 27. Kuma na kasance haka har shekara biyu. Ban taba tsammani cewa hakan zai faru ba!

“Ina gani abin da ya sa na yi nasara ba irin abincin da nake ci kawai ba, amma canje-canjen da na yi a salon rayuwata ne.”—Catherine, ’yar shekara 18.