Koma ka ga abin da ke ciki

Koma secondary menu

Shaidun Jehobah

Hausa

Ba Zan Iya Daina Tunanin Yin Jima’i Ba

Ba Zan Iya Daina Tunanin Yin Jima’i Ba

Abin da za ka iya yi

Ka zabi abokanka da kyau. Sa’ad da abokanka da ’yan ajinku suka fara tadin yin iskanci, idan ka sa baki hakan zai kara sa dada yin tunaninsa. A yawancin lokaci, za ka guje wa irin tadin nan ba tare da ka nuna cewa kai mai adalci ba ne domin hakan zai sa a yi maka ba’a.

Za ka kyale kwayoyin cutar kwamfuta su shiga kwamfutarka? To me zai sa ka kyale tunanin da bai da kyau ya shiga zuciyarka?

Ka guje wa nishadi marar kyau. Yawancin nishadina zamani ana shirya su ne don su ta da sha’awar yin iskanci. Mene ne gargadin da Littafi Mai Tsarki ya bayar? “Bari mu tsarkake kanmu daga dukan kazamtar jiki da ta ruhu, muna kāmala tsarki cikin tsoron Allah.” (2 Korintiyawa 7:1) Ka guji duk wani nishadi da zai motsa sha’awar yin iskanci.

Ka tuna cewa: Sha’awar yin jima’i kansa ba laifi ba ne. Balle ma, Allah ya halicci namiji da mace su yi sha’awar junansu, kuma yin jima’i cikin aure daidai ne. Saboda haka, sa’ad da ka ji sha’awar yin jima’i, kada ka yi tunanin cewa kai dai wani dan iska ne ko kuma cewa ba za ka taba kasancewa da tsarki a dabi’a ba.

Gaskiyar al’amarin shi ne: Kana iya zaban abin da za ka yi tunani a kansa. Za ka iya kasance da tunani da kuma halin kirki idan kana so!