Koma ka ga abin da ke ciki

Shaidun Jehobah

Ka Zabi Yare Hausa

Kamar Na Daina Makaranta

Kamar Na Daina Makaranta

Ga abin da ya kamata ka yi tunaninsa

Dokar kasarku ta bukaci a yi makaranta na akalla shekara nawa ne? Ka gama shekarun? Idan ka yi watsi da gargadin Littafi Mai Tsarki game da “zaman biyayya da ikon masu-mulki” kuma ka bar makaranta kafin ka kammala, to ka bar makarantar ke nan a hanya.—Romawa 13:1.

Ka cim ma burinka na ilimi kuwa? Wadanne buri ne kake so iliminka ya taimaka maka ka cim ma? Ba ka sani ba? Kana bukatar ka sani! Idan ba haka ba, za ka zama kamar wani da ya shiga jirgi amma bai san inda za shi ba. Saboda haka, ka zauna tare da iyayenka kuma ku tattauna sashen nan na kasa “ Makasudaina Na Yin Karatu.” Idan ka bari kafin ka cim ma burinka na ilimi wanda kai da iyayenka ku ka tsara, to ka bar makarantar a hanya ke nan.

Me ya sa kake son ka bar makaranta? Watakila kana son ka taimaka wa iyalinka ko kuma ka yi aikin agaji. Wasu dalilai na son kai sune don ka guji jarrabawa ko kuma aikin makaranta da za ka yi a gida. Matsalar ita ce ka san ainihin abin da ke zuciyarka, mai kyau ne ko na son kai. Idan ka daina don ka guje wa matsaloli ne, lallai za ka sha mamaki.

Barin makaranta tun ba ka gama ba yana kama ne da sauka a jirgin kasa kafin ka kai inda za ka. Kila jirgin ba dadi, kuma fasinjojin ba su da kirki, amma idan ka yi tsalle daga jirgin, lallai ba za ka kai inda ka yi niyyar zuwa ba, za ma ka ji wa kanka rauni. Hakazalika, idan ka bar makaranta tun ba ka gama ba, zai yi wuya ka sami aikin yi. Idan ma ka samu, watakila ba za ka samu albashi mai tsoka ba da za ka samu idan ka gama makaranta.

Maimakon ka daina makaranta, ka hakura ka fuskanci matsalolin da ke makarantar. Idan ka yi haka za ka kasance da jimiri kuma za ka kasance a shirye domin fuskantar kalubale a lokacin da ka soma aiki.

 Makasudaina Na Yin Karatu

Dalili na farko na samun ilimi shi ne domin ka sami aikin yi da zai iya taimaka maka da kuma iyalinka. (2 Tasalonikawa 3:10, 12) Ka tsai da shawara game da irin aikin da za ka so ka yi da kuma shekarun da za ka yi kana makaranta? Domin ka sani ko karatun da kake yi zai sa ka cim ma abubuwan masu kyau, ka amsa wadannan tambayoyi:

  • Wadanne halaye nake da su na kirki? (Alal misali, kana sha’ani da mutane kuwa? Kana son yin aiki da hannunka, kera abubuwa ko kuma gyaran abubuwa kuwa? Kana iya kokarinka ka magance matsaloli idan suka taso?)

  • Wadanne irin ayyuka ne za su sa na yi amfani da fasaha ta?

  • Wadanne irin aiki ake samu a inda nake da zama?

  • Wadanne abubuwa ne nake koya a makaranta yanzu da za su taimake ni samun aiki nan gaba?

  • Wadanne zabi na karatu da nake da su yanzu da za su taimake ni na cim ma makasudai na yadda ya kamata?

Ka tuna, burinka shi ne ka sauke karatu da ilimin da za ka yi amfani da shi. Saboda haka, kada ka zama dalibi na dindindin—wanda yake zama a “cikin jirgi” ya ki sauka don ya guji hakkin da ke kansa.