Koma ka ga abin da ke ciki

TAMBAYOYIN MATASA

Idan Ina da Wata Cuta Fa? (Sashe na 3)

Idan Ina da Wata Cuta Fa? (Sashe na 3)

 An san matasa da koshin lafiya da kuzari sosai. Amma wasu matasa ba su da wannan gatan saboda wani ciwo mai tsanani da ke ci masu tuwo a kwarya. Shin kana fuskantar irin wannan yanayin ne? Idan haka ne, watakila labaran V’loria da Justin da kuma Nisa, wasu matasa uku da Shaidun Jehobah ne za su karfafa ka. Ka lura da yadda suka jure da cututtuka masu tsanani da suke fama da su.

 V’loria

 Na kamu da wata cuta da ake kira fibromyalgia sa’ad da nake shekara 14. Da na kai shekara 20, sai na kamu da ciwon sanyin kashi, wato arthritis, da wani ciwo mai karya garkuwar jiki da ake kira lupus da kuma Lyme disease. A wannan yanayin, yana da wuya ka yi abubuwan da kake so don jikinka a mace yake kowane lokaci. A wasu lokuta, sai in nakasa daga kwonkwasona har zuwa kafafuwana. Saboda haka, na bukaci keken guragu.

 Abin da ya fi hakan muni shi ne damuwa ainun da nake yawan yi don ba na iya yin wasu abubuwa da ba su taka kara sun karya ba, kamar rubutu ko kuma bude murfin galan. Zan ga yara suna tafiya kuma in soma tunanin me ya sa yin hakan yake da wuya a gare ni. Sai na ji kamar ban da amfani.

 Abin farin ciki shi ne dangina da kuma ’yan’uwa daga ikilisiyar Shaidun Jehobah da nake tarayya da su suna taimaka min. ’Yan’uwa daga ikilisiya sukan ziyarce ni kuma hakan ya sa ba na jin kadaici sosai. Wasu sukan gayyace ni zuwa liyafa, duk da cewa hakan ya kunshi dora ni a kan kekena, shigar da ni cikin mota, da kuma saukar da ni.

 Tsofaffi da ke cikin ikilisiya sun taimaka min sosai don sun fahimci yanayin da mai rashin lafiya yake ciki. Sun taimaka min in amince da yanayin da na sami kai na a ciki kuma in daina bakin ciki saboda abubuwan da ba na iya yi. Babu abubuwan da suka fi sa ni farin ciki kamar halartan taro da kuma fita wa’azi. (Ibraniyawa 10:25) A wadannan lokutan, na fahimci cewa ban bambanta da sauran mutane ba, duk da cewa ina rashin lafiya.

 Na tuna cewa Jehobah yana yi mana tanadin abin da muke bukata don mu jimre. Alal misali, Littafi Mai Tsarki ya ce ko da jikinmu yana lalacewa, halittarmu na ciki zai iya “sabuntuwa yau da gobe.” (2 Korintiyawa 4:16) Hakika, hakan ne nake ji!

 Ka yi tunani akan wannan: Idan kana fama da wani ciwo mai tsanani, me ya sa yake da muhimmanci ka rika tarayya da mutane? Idan kana da koshin lafiya, ta yaya za ka taimaka wa wanda yake rashi lafiya?—Misalai 17:17.

 Justin

 Na fadi kuma na kasa tashi. Sai na jin zafi a kirjina kuma na kasa motsi. Aka kai ni dakin jinyar gaggawa a guje. Da farko, likitoci sun kasa sani abin da yake damuna. Amma bayan abin ya faru sau da yawa, sai suka yi bincike kuma suka gano cewa na kamu da wata cuta da ake kira Lyme disease.

 Wannan cutar ta shafi tsarin jijiyoyina. Har yanzu, nakan yi rawan jiki, a wani lokaci ba na iya dainawa duk da cewa shekaru da dama sun wuce tun lokacin da aka gano cutar. Akwai kwanakin da jikina zai rika yin ciwo, har da yatsuna kuma ba na iya motsa su. Kamar dai gababuwana sun yi tsatsa.

 Na soma tunani cewa ‘Da yake ni matashi ne, bai kamata in yi ciwo ba,’ kuma hakan yana sa ni bakin ciki. Nakan yi kuka kuma in tambayi Allah “Me ya sa nake fuskanta wannan yanayin?” Har na ji kamar Allah ya yi watsi da ni. Amma sai na tuna da Ayuba da aka ambata a cikin Littafi Mai Tsarki. Ayuba bai san dalilin da ya sa ya fuskanci matsalolin da ya fuskanta ba, duk da haka, ya kasance da aminci ga Allah. Idan har Ayuba zai iya yin hakan duk da matsaloli masu tsanani da ya fuskanta, ni ma zan iya yi.

 Na sami taimako sosai daga dattawan da ke ikilisiyarmu. Suna ziyara na a kowane lokaci don su san yadda nake ji. Wani dattijo ya gaya min in kira shi a duk lokacin da nake son wanda zan yi hira da shi. Ina godiya ga Jehobah kullum saboda wadannan abokai kirki!—Ishaya 32:1, 2.

 A wani lokaci sa’ad da muke fama da wani ciwo mai tsanani, mukan manta cewa Jehobah ya san yanayin da muke ciki. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ka zuba nawayarka bisa Ubangiji, shi kuma za ya taimake ka.” (Zabura 55:22) Abin da nake yunkurin yi kullum ke nan.

 Ka yi tunani akan wannan: Ta yaya mutanen da suke kaunarka za su iya taimaka maka ka jure da rashin lafiya?—Misalai 24:10; 1 Tasalonikawa 5:11.

 Nisa

 Sa’ad da nake wajen shekara 15, likita ya gaya min cewa na kamu da Marfan syndrome, wata cuta mai kashe gabobin jiki. Marfan syndrome zai iya shafan zuciyarka da idanunka da wasu gabobi masu muhimmanci. Ba kullum ba ne nake jin zafi, amma idan jikina ya soma ciwo, nakan ji radadi ba kadan ba.

 Na yi kuka sosai sa’ad da likita ya gaya min cewa na kamu da cutar. Na damu cewa ba zan iya yin abubuwan da nake son yi ba. Alal misali, ni mai son yin rawa ne, sanin cewa ciwon ba zai bar ni in yi hakan ba, har ma zai hana ni tafiya da kafa, ya sa na soma fargaban abin da zai faru a nan gaba.

 Yayata ta taimaka min sosai. Ta sa na daina jin tausayin kaina. Ta ce kada in rika fargaba don hakan zai sa ni bakin ciki sosai. Ta karfafa ni in nace a yin addu’a don Jehobah ne kadai ya san ainihin abin da nake fuskanta.—1 Bitrus 5:7.

 Nassin da ya karfafa ni shi ne Zabura 18:6 da ta ce: “A cikin kuncina na yi kira ga Ubangiji, Na tada murya zuwa ga Allahna: Ya ji muryata daga cikin haikalinsa, Kukana kuma da na yi a gabansa ya shiga kunnuwansa.” Wannan ayar ta taimaka min in fahimta cewa sa’ad da na yi addu’a ga Jehobah kuma na roke shi ya ba ni karfin jurewa, zai ji ni kuma ya taimaka min. Yana shirye ya karfafa ni a kowane lokaci.

 Na koyi cewa yin bakin ciki saboda wata matsala da muke fuskanta ba laifi ba ne don mu ’yan Adam ne. Amma kada mu bar matsalar ta damu sosai har hakan ya shafi dangantakarmu da Allah. Ba shi ne yake jawo mana matsalolin ba, kuma ba zai yi watsi da mu ba idan mu saka shi kan gaba a rayuwarmu.—Yakub 4:8.

 Ka yi tunani akan wannan: Shin Allah ne yake haddasa matsalolinmu?—Yakub 1:13.