Koma ka ga abin da ke ciki

Koma secondary menu

Shaidun Jehobah

Hausa

TAMBAYOYIN MATASA

Ta Yaya Zan Yi Kokarin Bin Dokokin Iyayena?

Ta Yaya Zan Yi Kokarin Bin Dokokin Iyayena?

Watakila ka san matasa tsaranka wadanda suke dawowa gida lokacin da suke so, su sanya tufar da suke so, su yi yawo da duk abokan da suke so kuma su je duk inda suke so. Kila ma iyayensu sun takure ba su san abin da yaransu suke yi ba.

Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa irin wannan renon yara ba zai yi nasara ba. (Misalai 29:15) Yawancin rashin kauna da ake gani cikin duniya a yau daga mutane masu son kansu ne domin iyalai ne da ba a koya musu kamewar kai ba.2 Timotawus 3:1-5.

Maimakon ka yi kishin matasa da aka kyale su su yi abin da suke so, ka yi kokarin ganin dokokin iyayenka tabbacin kaunarsu ce gare ka. Yadda suke ba da dokokin kariya suna yin koyi ne da Jehobah Allah, wanda ya ce wa mutanensa:

“Ni sanarda kai, ni koya maka cikin tafarkin da za ka bi: da idona a kanka zan ba ka shawara.”—Zabura 32:8.