Koma ka ga abin da ke ciki

TAMBAYOYIN MATASA

Ta Yaya Zan Bayyana Ra’ayina Game da Yin Jima’i?

Ta Yaya Zan Bayyana Ra’ayina Game da Yin Jima’i?

“Tabdi, wai har yanzu ba ki san namiji ba?”

Idan kina son ki ba da amsa kuma amsar e ce, za ki so ki fadi hakan da gaba gadi? Wannan talifin zai taimaka miki ki yi hakan!

 Me ake nufi idan aka ce mace budurwa ce?

 Budurwa mace ce da ba ta taba yin jima’i ba.

 Amma ba lallai ba ne sai namiji ya kwana da yarinya kafin a ce ta yi jima’i. Wasu za su iya cewa namiji bai taba kwana da su ba, saboda haka su budurwai ne, amma sun riga sun yi lalata iri-iri.

 Kalmar nan “jima’i” yana nufin yin jima’i ta baki ko yin luwadi ko kuma yin wasa da al’aura don ta da sha’awa.

 Gaskiyar al’amarin: Mutanen da sun riga sun yi jima’i ko luwadi ko kuma sun yi wasa da al’aurar wasu ba budurwai ba ne.

 Mene ne Littafi Mai Tsarki ya fada game da yin jima’i?

 Littafi Mai Tsarki ya ce ya kamata yin jima’i ya kasance tsakanin mata da miji da suka yi aure ne kadai. (Misalai 5:​18) Saboda haka, wanda yake so ya faranta wa Allah rai ba zai yi jima’i ba har sai ya yi aure.​—1 Tasalonikawa 4:3-5.

 Wasu sun ce abin da aka rubuta a cikin Littafi Mai Tsarki tsohon yayi ne kuma bai dace da wannan zamanin ba. Amma ku tuna cewa zamaninmu yana cike da matsaloli kamar kisan aure da cikin shege da kuma cututtuka da ake yadawa ta wurin jima’i. Hakika babu wata shawara mai kyau game da dabi’a da za mu iya samu daga wannan duniyar Shaidan!​—1 Yohanna 2:15-17.

 Idan kin yi tunanin ka’idodin da Littafi Mai Tsarki ya bayar a kan dabi’a, za ki ga cewa suna da amfani sosai. Alal misali: A ce wani ya ba ki kyautar $1,000 (dalla dubu daya). Za ki jefar da kudin wa duk wanda yake so ya dauka?

 Haka ma yake da batun jima’i. Sierra, wata ’yar shekara 14 ta ce: “Ba na so wani namijin da mai yiwuwa ba zan ma tuna da sunansa ba ya bata budurcina.” Tammy wata ’yar shekara 17 ta ce: “Jima’i kyauta ce ta musamman da bai kamata a yi banza da shi ba.”

 Gaskiyar al’amarin: Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa bai kamata wadanda ba su yi aure ba su yi jima’i ko kuma su sa hannu a dabi’u marasa kyau.​—1 Korintiyawa 6:​18; 7:​8, 9.

 Mene ne ra’ayinki?

  •   Kin gaskata cewa abin da Littafi Mai Tsarki ya fada game da jima’i yana da kyau ko kuma yana da wuyan bi?

  •   Kin yarda cewa ba laifi ba ne mutane biyu da ba su yi aure ba su yi jima’i don suna son juna sosai?

 Bayan da matasa da yawa sun yi tunani a kan wannan batun, sukan ce sun fi so su kiyaye budurcinsu kuma su zama da dabi’u masu mai kyau. Ba sa yin da-na-sani game da shawarar da suka dauka kuma ba sa ji kamar an cuce su. Ga abin da wasu suka ce:

  •  Emily ta ce: “Ina farin ciki cewa ni budurwa ce! Guje wa ciwon zuciya da azabar da ke tattare da yin jima’i kafin aure ba laifi ba ne.”

  •  Elaine ta ce: “Na yi farin cikin sanin cewa ban taba yin jima’i da wani namiji ba kuma ban taba kamuwa da cutar da ake samu ta wurin yin jima’i ba.”

  •  Vera ta ce: “Na sha jin ’yammata da yawa tsarana da wadanda suka girme ni suna nadama don ba su jira sai bayan aure kafin su yi jima’i ba, don haka ba na son in yi irin wannan kuskuren.”

  •  Deanne ta ce: “Na san mutane da yawa da suka yi jima’i kafin aure kuma hakan ya jawo musu bakin ciki mai tsanani don sun yi banza da budurcinsu ko kuma sun yi lalata da mutane da yawa. A ganina, wannan ba rayuwa ba ce.”

 Gaskiyar al’amarin: Kina bukatar ki san matakin da za ki dauka tun kafin ki fuskanci matsi ko jarabar yin jima’i.—Yakub 1:​14, 15.

 Ta yaya za ki bayyana wa mutane abin da kika yi imani da shi?

 Me ya kamata ki fada idan wani yana so ya san ra’ayinki game da jima’i? Wannan ya dangana ga yanayin.

 Corinne ta ce: “Idan mutum yana zolayata ne kawai, ba zan yi shiru ba. Zan ce, ‘Babu ruwanka’ kuma zan bar wurin.”

 David ya ce: “A makaranta wasu suna jin dadin cin zalin mutum don su yi masa dariya kawai. Idan dalilin da ya sa suke mini tambayar ke nan, to, ba zan ma amsa su ba.”

 Ka sani? A wasu lokatai, Yesu yakan yi shiru maimakon ya ‘amsa’ masu tuhumarsa.​—Matta 26:62, 63.

 Amma idan wadda take tambayarki tana yin hakan da gaske ne kuma cikin ladabi fa? Idan kika ga cewa ta yi imani da Littafi Mai Tsarki, za ki iya karanta mata 1 Korintiyawa 6:​18, da ya ce wanda ya yi jima’i kafin aure yana yi wa jikinsa zunubi ko kuma yana lalata jikinsa.

 Ko da kin yi kaulin Littafi Mai Tsarki nan da nan ko ba ki yi ba, yana da muhimmanci ki yi magana da gaba gadi. Ki tuna cewa ya kamata ki yi alfahari da matakin da kika dauka na kasancewa da dabi’a mai kyau.​—1 Bitrus 3:​16.

 Jill ta ce: “Idan kika ba da amsa da gaba gadi, hakan zai nuna cewa ba ki yi shakkar abin da kika gaskata ba kuma kin san cewa matakin da kika dauka daidai ne, ba abin da aka ce ki yi kawai ba.”

 Gaskiyar al’amarin: Idan kin tabbata da matakin da kika dauka game da jima’i, ba zai yi miki wuya ki bayyana ma wasu ba. Hakan na iya yin tasiri mai kyau a kansu. Melinda wata ’yar shekara 21 ta ce: “Abokan aikina suna yaba mini domin ban lalata kaina ba. Suna ganin hakan yana da kyau sosai domin a ganinsu na kame kaina kuma ina da dabi’a mai kyau.”

 Taimako! Idan kina bukatar taimako don ki dauka mataki mai kyau game da yin jima’i, ki sauko da shafin rubutun nan “Yadda Za Ka Bayyana Imaninka Game da Jima’i.” Kari ga haka ki duba littafin nan Questions Young People Ask​—Answers That Work.

  •    Babi na 24 na littafin nan Questions Young People Ask—Answers That Work, Volume 1 mai jigo “Will Sex Improve Our Relationship?

  •    Babi na 5 na littafin nan Questions Young People Ask​—Answers That Work, Volume 2 mai jigo “Why Stay a Virgin?

 Victoria ta ce: “Ina son bayanin da aka yi a cikin littattafan nan Young People Ask​—Answers That Work, Volume 1 da Volume 2. Alal misali, shafi na 187 a cikin Young People Ask​—Answers That Work, Volume 1, an kwatanta yin jima’i kafin aure da sarka mai tsada sosai da aka jefar. Hakan zubar da mutuncinka ne. Shafi na 177 ya bayyana cewa yin jima’i kafin mutum ya yi aure yana kama da amfani da wani kayan ado mai kyau a matsayin tabarma. Amma kwatancin da na fi jin dadinsa a cikin littafin shi ne wanda yake shafi na 54 na Young People Ask​—Answers That Work, Volume 2. Bayanin da ke cikin kwatancin shi ne: ‘Yin jima’i kafin mutum ya yi aure yana kama da bude kyautar da ake so a ba ka tun ba a ba ka ba. Kamar dai kina satar abin da ba na ki ba ne, wato na abokin aurenki.