Koma ka ga abin da ke ciki

Shaidun Jehobah

Ka Zabi Yare Hausa

Ba Na Dacewa da Mutane

Ba Na Dacewa da Mutane

Abin da za ka iya yi

Na Daya, ka san irin mutanen da ba ka dacewa da su.

Shekaru:

Ba na da ce da . . .

 • tsarana

 • manyan matasa

 • manyan mutane

Kwarewa:

Ba na dacewa da . . .

 • ’yan wasa

 • masu baiwa

 • masu ilimi

Hali:

Ba na dacewa da . . .

 • masu gaba gadi

 • masu farin jini

 • ’yan rukuni

Na biyu, ka zabi yadda ka ke ji idan kana tare da irin mutanen da ka ambata a sama din nan.

 • Nakan yi kamar halin mu daya da su ko kuma ina iya abin da suka iya.

 • Nakan yi banza da zancen da suke yi kuma na mai da hankali a kan nawa zancen.

 • Nakan zauna shuru kuma in nemi zarafin barin wajen.

Na uku, ka dauki mataki! Ba a kowane lokaci ne mutane za su zo wajenka ba; wasu lokaci kai ma sai ka je wajensu. (Filibiyawa 2:4) Ta yaya za ka iya yin haka?

Ka nemi yin abota da wanda ba tsararka ba. Ka tambayi kanka: Me ya sa zan tsaya yin abota da tsarana kawai sa’an nan kuma in ce ban da abokai? Hakan kamar kasancewa a cikin ruwa ne da sabulu a ido!

Mahaifiyata ta karfafa ni na rika yin tadi da wasu da suka manyanta. Ta ce zan yi mamakin ganin cewa ina da ra’ayi daya da su. Gaskiyarta, yanzu ina da abokai da yawa!”—Helena, 20.

Ka koyi yin tadi da mutane. Sirrin shi ne (1) ka saurara, (2) ka yi tambayoyi, kuma (3) ka nuna kana son mutane da gaske.—Yakub 1:19.

Ina kokarin kasa kunne maimakon cika magana. Kuma idan na yi magana, nakan yi kokari kaskantar da kaina kuma in girmama wasu.”—Serena, 18.

Idan mutum yana magana game da abin da ban sani ba, nakan ce ya bayyana mini, kuma hakan zai sa ya kara yi mini bayani.”—Jared, 21.

Ni mai kunya ce, saboda haka, sai na dāge kafin in yi tadi da mutum. Amma idan kana son abota, wajibi ne ka so mutane. Hakan ya sa ni yin magana da mutane.”—Leah, 16.