Koma ka ga abin da ke ciki

TAMBAYOYIN MATASA

Shin Mu Abokai Ne Ko Kuma Masoya?​—Sashe na 1

Shin Mu Abokai Ne Ko Kuma Masoya?​—Sashe na 1

 Kina son sa sosai kuma kin tabbata cewa shi ma yana son ki. Kuna tura wa juna sako kullum kuma kuna kasancewa tare a duk lokacin da ake liyafa . . .  kuma wasu sakon da yake tura miki ya nuna cewa yana son ki.

 Saboda haka, sai kika yanke shawarar tambayar sa wace irin dangantaka ce ke tsakaninku, don kina son ki san ko yana son ki. Abin da ya gaya miki shi ne, “ke abokiyata ce kawai.”

 Yadda za ku ji

 Jasmine ta ce: “Na yi bakin ciki sosai kuma na ji haushin sa da kuma kaina! Mun dade muna tura wa juna sakonni, kuma ya nuna cewa yana sona. Saboda haka na soma son sa.”

 Richard ya ce: “Ni da ita ’yan rakiya ne wa wasu masoya. A wasu lokatai, ji nake kamar dukanmu masoya ne. Ni da ita muna yin hira sosai, daga haka muka soma tura wa juna sakonni. Na yi bakin ciki sosai lokacin da ta gaya mini cewa ta dauke ni a matsayin abokinta ne kawai kuma tana da saurayi.”

 Tamara ta ce: “Akwai wani yaron da yake tura mini sako kullum kuma a wasu lokatai dukanmu muna wa juna soyayya. Amma da na gaya masa cewa ina son sa, sai ya yi dariya kuma ya ce, ‘Ba na son in soma soyayya da kowa yanzu!’ Hakan ya sa ni bakin ciki na dogon lokaci.”

 Gaskiyar al’amari: Dole ne ka yi ko ki yi bakin ciki da kuma fushi idan wanda kike tunanin yana son ki ba ya son ki. Kuma za ki ko ka ga kamar ta ci amanarka. Wani matashi mai suna Steven ya ce: “Na yi bakin ciki da hakan ya faru da ni kuma na ji zafi sosai. Don haka, ya dauki dogon lokaci kafin na soma amincewa da mutane.”

 Abin da ya sa hakan yake faruwa

 Tura sakonni da kuma hira ta intane yana sa mutane su soma son wanda da gaske ba ya son su. Ku yi la’akari da abin da wasu matasa suka ce.

 Jennifer ta ce: “Wani yakan tura miki sako ne kawai don ba shi da aikin yi, ke kuma za ki dauka cewa son ki yake yi. Kari ga haka, idan kullum yana tura miki sako, za ki iya soma jin cewa yana son ki sosai.”

 James ya ce: “Watakila daya daga cikinku yana so ku zama masoya, dayan kuma yana neman wanda zai yi hira da shi ne kawai, ko kuma yana tura sako ne don ya nuna cewa shi ma yana da abokai ’yammata da yawa.”

 Hailey ta ce: “Idan kika tura sako kamar ‘sai da safe,’ ana iya dauka sakon ta soyayya ce, amma ba a san cewa watakila gaisuwa ce kawai ba.”

 Alicia ta ce: “Idan kika tura wa wani alamar fuskar da ke murmushi, kamar kina nufin cewa, ‘Ina da kirki’ ko kuma ‘kwarkwasa nake yi.’ A wasu lokatai, wanda kike tura wa sakon yana ganin kamar kina masa kwarkwasa ne.”

 Gaskiyar al’amarin: Kada ki ko ka dauka cewa tana son ka don tana sauraranka.

  Yin hakan ba shi da sauki! Littafi Mai Tsarki ya ce: “Zuciya ta fi komi rikici cuta gareta ƙwarai irin ta fidda zuciya.” (Irmiya 17:9) Zuciyarku za ta iya sa ku soma soyayya da a tunanin ku ne kawai amma ba zahiri ba ce kuma sa’ad da kuka fahimci hakan, soyayyar za ta bace.

 Abin da za ku iya yi

  •   Ku bincika kanku. Ku dauki lokaci don ku yi bincike a kan dangantakar da ke tsakaninku. Ku tambayi kanku, ‘Mene ne ya tabbatar mini cewa wannan mutumin yana bi da ni dabam da yadda yake bi da wasu?’ Kada ku bar yadda kuke ji ya sa ku kasa yin tunani sosai.​—Romawa 12:1.

  •   Ku yi tunani. Maimakon ku rika tunani a kan dalilin da ya sa kuke ganin cewa ku masoya ne, ku fi mai da hankali ga abubuwan da suka sa kuke shakkar hakan. Kada ka ko ki dauka cewa saboda kina son wani shi ma yana son ki.

  •   Ku zama masu hakuri. Ka ko ki jira har sai ya fito fili ya ce yana son ki. Kafin wannan lokacin, kada ki bata lokacinki kina tunanin soyayya da ba ki da tabbacin hakan.

  •   Ku rika gaya wa kanku gaskiya. Littafi Mai Tsarki ya ce: Akwai “lokacin magana.” (Mai-Wa’azi 3:7) Idan kuna son ku san ko wani yana son ku da gaske, zai dace ku tambaye shi. Wata matashiya mai suna Valerie ta ce: “Idan ba soyayya kuke yi ba, gwamma ku sani tun da wuri maimakon ku dauki dogon lokaci kafin ku san cewa ashe ba soyayya kuke yi ba. Hakan ya fi zafi da kuma sa mutum bakin ciki.”

 Gaskiyar al’amarin: Littafin Misalai 4:23 ta ce: “Ka kiyaye zuciyarka.” Idan kina ko kana son wata, zai dace ka tambaye ta ko ita ma tana sonka. Barin irin wannan soyayya ta kahu a zuciyarku yana kama da yin shuka a kan dutse mai karfi.

 Idan ka ko kika tabbatar da cewa yana sonki, kuma kin kai ki soma fita zance, ke ce za ki yanke shawara ko za ki yi soyayya da shi. Ku tuna cewa, kafin aure ta kasance da inganci wajibi ne mata da miji sun kafa makasudi irin daya a ibadarsu ga Jehobah, kuma suna gaya wa juna gaskiya. (1 Korintiyawa 7:39) Hakika, kafin namiji da tamace su yi aure, suna somawa ne da abokanta kuma su ci gaba da zama abokai bayan aure.​—Misalai 5:18.