TAIMAKO DON IYALI | AURE
Zai Dace Waɗanda Ba Su Yi Aure Ba Su Zauna Tare?
Akwai maza da mata da yawa da suke zama ba tare da yin aure ba. Wasu sukan yi hakan ne don su ga ko sun dace da juna, kuma suna ganin yin hakan zai taimaka musu su zauna lafiya bayan sun yi aure. Amma ya dace namiji da ta mace su zauna tare ba tare da yin aure ba?
Ga tambayoyin da za mu tattauna a talifin nan
Mene ne Littafi Mai Tsarki ya ce?
Littafi Mai Tsarki ya haramta yin jimaꞌi kafin aure. Alal misali, ya ce: “Ku guji yin lalata.” (1 Tasalonikawa 4:3; 1 Korintiyawa 6:18) Hakan ya nuna cewa bai kamata namiji da ta mace da ba su yi aure ba su yi jimaꞌi, ko da suna da niyyar yin aure daga baya. a Abin da ke Littafi Mai Tsarki zai iya taimaka wa mutane su guji munanan sakamakon da namiji da ta mace da ba su yi aure ba za su iya samu, kamar cikin shege da dai sauransu.
Allah ne ya fara ɗaura aure. A lokacin da ya yi hakan, ya ce: “Mutum zai bar babansa da mamarsa ya manne wa matarsa, biyun su zama ɗaya.” (Farawa 2:24) Idan namiji da ta mace suka yi wa juna alkawari a ranar aurensu, hakan zai iya sa a sami zaman lafiya a iyalin.
Shin zaman tare zai sa ku zauna lafiya bayan kun yi aure?
Wasu suna ganin amsar e ce. Suna ganin yayin da suke ayyukan gida tare kuma suna ganin halayen juna, hakan zai sa su fahimci juna da kyau. Amma abin da ya fi taimaka wa maꞌaurata shi ne tuna da alkawarin da suka ɗauka a ranar aurensu.
Mene ne zai taimaka wa mace da namiji su manne wa juna, ko da daɗi ko ba daɗi? Riƙe amanar aure da kuma yin ƙoƙarin magance matsaloli ne zai taimaka. Amma idan mace da namijin suna zama ba tare da yin aure ba, hakan zai iya sa ba za su daraja dagantaka da ke tsakaninsu ba kuma za su iya rabuwa a duk lokacin da suka ga dama.
Gaskiyar batun: Idan mutane suna zama ba tare da yin aure ba, hakan ba zai sa su ɗauki aure da daraja ba, kuma rabuwa ba zai yi musu wuya ba.
Ƙaꞌidar Littafi Mai Tsarki: “Gama duk abin da mutum yake shukawa, shi zai girba.”—Galatiyawa 6:7.
Shin zaman tare zai taimaka muku ku tara kuɗi?
Wasu suna ganin amsar e ce. Wani binciken da aka yi a Amirka ya nuna cewa, mutane huɗu cikin goma da suka soma zama tare kafin su yi aure sun yi hakan ne don suna ganin zai taimaka musu su tara kuɗin aure. Amma, binciken ya nuna cewa bayan sun zauna tare na ɗan lokaci, ba su iya yin auren ba domin rashin isasshen kuɗi.
Ban da haka ma, zama ba tare da yin aure ba yana iya jawo wasu munanan sakamako musamman ga mata. Alal misali, idan namiji da ta mace da suke zama ba tare da yin aure ba suka rabu, a yawancin lokuta matan ne suke ɗaukan nauyin renon yara.
Gaskiyar batun: Matsalolin da ake fama da su idan aka soma zama ba tare da yin aure ba sun fi amfanin da ake tunanin samu a ciki.
Ƙaꞌidar Littafi Mai Tsarki: ‘Ni ne Yahweh Allahnku, wanda yake koya muku domin amfanin kanku.’—Ishaya 48:17.
Shin zaman tare zai taimaka muku ku guji auran wanda bai dace da ku ba?
Wasu suna ganin amsar e ce. Amma littafin nan Fighting for Your Marriage ya ce, “mutanen da suka soma zama kafin su yi aure ba su san cewa bayan wani lokaci, zai iya yi musu wuya su rabu ko da ba sa jin daɗin zama da juna.” Me ya sa? Masu bincike sun gano cewa, ko da waɗanda suke zama tare sun fahimci cewa ba su dace da juna ba, sukan ci-gaba da zama domin wasu abubuwa da suka yi tare. Alal misali, wataƙila sun sayi dabba tare, ko sun biya kuɗin gida tare, ko kuma macen ta riga ta yi ciki. Saboda haka, maimakon su rabu sukan ci-gaba da zama har su yi aure.
Gaskiyar batun: Maimakon taimaka wa mutum ya yanke shawara mai kyau, zama ba tare da yin aure ba zai iya sa mutum ya maƙale da wanda baya so.
Ƙaꞌidar Littafi Mai Tsarki: “Mai hankali yakan ga hatsari, ya kauce, amma marar tunani yakan sa kai, ya sha wahala.”—Karin Magana 22:3.
Mene ne zai fi taimakawa?
Zai yiwu mu guje wa munanan sakamakon da ke tattare da zama ba tare da yin aure ba kuma mu zauna lafiya bayan aure. Mene ne zai taimaka? Bin ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki game da aure. Zai dace ka ɗau lokaci don ka fahimci wanda kake so ka aura da kyau kafin ku yi aure. Zai fi kyau ka auri wanda raꞌayi da imaninku ɗaya ne, maimakon ka mai da hankali a kan kyaun fuska ko siffar jiki.
Littafi Mai Tsarki na ɗauke da shawarwari da za su taimaka maka ka yi shiri don ka ji daɗin aurenka. b Alal misali, akwai ƙaꞌidodin da za su taimaka maka . . .
ka guji cin amanar aboki ko abokiyar aurenka
ka zama mutumin kirkin da zai riƙe amana a aure
ka gane alamun da suke nuna cewa ba ku dace da juna ba tun kuna fita zance
Don samun ƙarin bayani game da irin batutuwan nan, ka duba sashen “Aure da Iyali” a jw.org/ha.
Ƙaꞌidar Littafi Mai Tsarki: “An rubuta dukan Nassi ta wurin ruhun Allah.”—2 Timoti 3:16.
a Ka duba talifin nan “Does Romantic Love Justify Premarital Sex?”
b A wasu wurare, iyaye ne suke zaɓa wa yaransu wanda za su aura. Idan haka ne, Littafi Mai Tsarki zai taimaka wa iyayen su zaɓi wanda yake da halayen kirki.

