Koma ka ga abin da ke ciki

TAIMAKO DON IYALI

Ku Tattauna da Yaranku Game da Shan Giya

Ku Tattauna da Yaranku Game da Shan Giya

 Alexander ya ce: “’Yarmu tana shekara shida sa’ad da muka tattauna batun shan giya da ita. Mun yi mamaki cewa ta riga ta san abubuwa da yawa game da giya.”

 Abin da ya kamata ka sani

 Yana da muhimmanci a tattauna da yara game da shan giya. Kada ka jira har sai yaranka sun zama matasa kafin ka tattauna da su. Wani mai suna Khamit a Rasha ya ce: “Ina bakin ciki cewa ban tattauna da danmu tun yana karami game da shan giya ba. Bayan abubuwa sun riga sun bace ne na koyi cewa yin hakan yana da muhimmanci. Na gano cewa danmu ya soma shan barasa a kai a kai tun yana shekara 13.”

 Me ya sa ya kamata hakan ya dame ka?

  •   Abokan aji da masu talla da kuma talabijin sukan sa yaronka ya kasance da ra’ayin cewa shan giya abu ne mai kyau.

  •   Bincike da Cibiyoyin Kula da Cuta da kuma Rigakafi suka yi ta nuna cewa a Amirka, yaran da ba su kai shekarar shan giya ne suke shan kashi 11 na giya da ake sha a kasar.

 Saboda haka, ma’aikatan kiwon lafiya sun gaya wa iyaye su koyar da yaransu tun suna kanana game da hadarurrukan da ke tattare da shan giya. Ta yaya za ka iya yin hakan?

 Abin da za ka iya yi

 Ka yi tunanin irin tambayoyin da yaronka zai iya yi maka. Yara suna son sanin abubuwa, amma matasa sun fi son sanin abubuwa. Saboda haka, yana da kyau ka shirya yadda za ka ba da amsa. Alal misali:

  •   Idan yaronka yana son ya san yadda dandanon giya take, kana iya gaya masa cewa giya ta dan yi kama da ruwan lemon tsami, biya [Beer] kuma tana da daci.

  •   Idan yaronka yana son ya dandana don ya san yadda giya take, kana iya gaya masa cewa barasa ta fi karfin yara sosai. Ka ambata yadda barasa ke shafan mutane: Giya tana sa mutum ya wartsake, amma yawan shan ta zai iya sa mutum jiri, ya soma yin abubuwa kamar marar hankali ko kuma ya soma yin maganganun da zai yi da-na-sani.—Karin Magana 23:29-35.

 Ka koyar da kanka. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Mai hankali ya san abin da yake yi.” (Karin Magana 13:16) Kana bukatar ka san yadda giya take shafan mutane da kuma dokokin da kasarku take bi game da shan giya. Hakan zai sa ka kasance a shirye ka taimaka wa yaranka.

 Ka soma tattauna batun. Wani mahaifi a Britaniya mai suna Mark ya ce: “Yara ba za su fahimci batun shan giya ba. Na tambayi yarona dan shekara 8 ko yana ganin ya dace a sha barasa ko a’a. Na sa hankalinsa ya kwanta kamar muna tadi, kuma hakan ya taimaka masa ya fadi ra’ayinsa.”

 Za ka taimaka wa yaranka sosai idan ka tattauna batun shan giya sau da yawa da su. Bisa ga shekarar danka, ka tattauna batun barasa sa’ad da kuke tattauna wasu abubuwa kamar mai da hankali sa’ad da yake ketare hanya da kuma batun jima’i.

 Ka kafa misali mai kyau. Yara suna kamar soso, suna tsotse dukan wani abin da ke wurin da suke. Kuma bincike ya nuna cewa iyaye ne suka fi rinjayar yaransu. Hakan yana nufin cewa idan kana shan giya don ka natsu ko kuma jimre matsaloli, yaranka za su koyi cewa giya ce take taimaka wa mutum ya magance alhini. Saboda haka, ka kafa musu misali mai kyau. Ka tabbata cewa kana shan giya a hanyar da ta dace.

Yaranka za su bi misalinka idan ka yi amfani da giya yadda ya dace