Koma ka ga abin da ke ciki

TAIMAKO DON IYALI | AURE

Yadda Ya Kamata Ka Yi Amfani da Na’ura

Yadda Ya Kamata Ka Yi Amfani da Na’ura

Yin amfani da na’ura zai iya sa ma’aurata su kusaci juna ko su yi nisa da juna. Yaya na’ura take shafan aurenka?

 Abin da ya kamata ka sani

  • Idan ma’aurata suna yin amfani da na’aura yadda ya kamata, hakan zai iya sa su kusaci juna. Alal misali, wasu suna amfani da shi don su tattauna da juna sa’ad da ba sa tare.

    Wani mai suna Jonathan ya ce: “Tura wa matarka dan sako cewa kana kaunarta ko kana tunaninta zai iya sa ku dada kusantar juna.”

  • Yin amfani da na’ura yadda bai kamata ba zai iya bata dangantakar da ke tsakanin ma’aurata. Alal misali, wasu ma’aurata suna amfani da na’urarsu a kowane lokaci kuma hakan yana sa ba sa iya ba matarsu ko mijinsu isasshen lokaci.

    Wata mai suna Julissa ta ce: “Na san akwai lokuta da maigidana zai so ya yi magana da ni da a ce ba na amfani da wayata.”

  • Wasu mutane sun ce za su iya tattaunawa da kyau da matarsu ko mijinsu yayin da suke amfani da na’urarsu. Amma wata masaniyar ilimin halin ’yan Adam mai suna Sherry Turkle ta ce, hakan “rudu ne game da yin ayyuka da yawa a lokaci daya.” Ko da yake wasu mutane sun dauka cewa yin ayyuka da yawa a lokaci daya yana da kyau, hakan ba gaskiya ba ne. Ta kara da cewa idan muna yin ayyuka da yawa a lokaci daya “ba za mu iya mai da hankali ga dukan abin da muke yi yadda ya kamata ba.” *

    Wata mai suna Sarah ta ce: “Nakan ji dadin tattaunawa da maigidana idan ba ya amfani da wayarsa. Idan yana magana da ni kuma yana amfani da wayarsa, sai in ji kamar wayarsa ce ta fi masa muhimmanci.”

Gaskiyar batun: Yin amfani da na’ura zai iya sa ma’aurata su kusaci juna ko su yi nisa da juna.

 Abin da za ka iya yi

Ka mai da hankali ga abin da ya fi muhimmanci. Littafi Mai Tsarki ya ce mu ‘zabi abin da ya fi kyau.’ (Filibiyawa 1:10) Ya kamata ka yi wa kanka wannan tambayar: ‘Shin ni da matata muna amfani da na’ura a lokacin da ya kamata mu yi cudanya da juna?’

Wani mai suna Matthew ya ce: “Ba dadi ka ga mace da namiji suna amfani da wayoyinsu sa’ad da suke cin abinci, kamar ba su damu da juna ba. Bai kamata mu mai da hankali ga na’urarmu har mu manta da abin da ya fi muhimmanci ba, wato dangantakarmu da mutane.”

Ka kebe lokaci. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ku mai da hankali kwarai ga zamanku. Kada ku zama kamar wawaye, sai dai kamar masu hikima. Ku yi amfani da kowane zarafi na yin kirki.” (Afisawa 5:​15, 16) Ka tambayi kanka, ‘Zan iya kebe lokacin karanta da kuma amsa sakonni da ba na gaggawa ba ne, a maimakon in amsa nan da nan a duk lokacin da sakon ya shigo?’

Wani mai suna Jonathan ya ce: “Nakan saita wayata yadda ba za ta dame ni ba, sa’an nan in amsa sakonnin da aka turo min a lokacin da ya fi dacewa. Da wuya a ce kowane kira ko sako ko imel ne kake bukatar ka amsa cikin gaggawa.”

Idan zai yiwu ka guji yin aikinka bayan ka tashi aiki. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ga kowane abu akwai lokacinsa.” (Mai-Wa’azi 3:⁠1) Ka yi wa kanka wadannan tambayoyin: ‘Ina barin aikina ya shafi cudanya da nake yi da iyalina domin ina amfani da wayata in yi aiki a gida? Idan haka ne, yaya matata take ji? Mene ne matata za ta ce game da wannan batun?’

Matthew ya ce: “Fasaha ta sa za mu iya yin aiki a duk inda muka ga dama da kuma lokacin da muke so. Nakan yi iya kokarina in guji yin amfani da wayata, ko da saboda aiki ne a duk lokacin da nake tare da matata.”

Ka tattauna batun yin amfani da na’ura da matarka. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Kada ka yi wa kanka kaɗai abu mai kyau, amma ka yi wa ɗan’uwanka kuma.” (1 Korintiyawa 10:24) Ka tattauna da matarka game da yadda kuke amfani da na’urarku da kuma canjin da ya kamata ku yi idan da bukata. Za ka iya yin amfani da shawarwari da aka bayar a wannan talifin.

Wata mai suna Danielle ta ce: “Ni da maigidana muna gaya wa juna gaskiya kuma idan dayanmu ya soma amfani da waya fiye da yadda ya kamata, muna fada wa mutumin hakan. Mun san cewa yin amfani da na’ura fiye da kima zai iya jawo matsala tsakaninmu, don haka, idan waninmu ya yi magana a kai, dayan yana saurara.”

Gaskiyar batun: Ka yi amfani da na’urarka yadda ya dace kuma kada ka bari ya yi iko a kanka.

^ sakin layi na 6 Daga littafin nan, Reclaiming Conversation​—⁠The Power of Talk in a Digital Age.