Koma ka ga abin da ke ciki

Ta Yaya Rayuwa Ta Soma?

Ta Yaya Rayuwa Ta Soma?

Wanne ne za ka zaba?

RAI YA SOMA NE TA WURIN . . .

  1. JUYIN HALITTA

  2. HALITTA

Wasu suna iya tunanin cewa dan kimiyya zai zabi “juyin halitta,” mai son addini kuma zai zabi “halitta.”

Amma ba haka yake a kullum ba.

Gaskiyar ita ce, mutane da dama da suka yi karatu sosai, har da ’yan kimiyya suna shakkar koyarwar juyin halitta.

Alal misali, Gerard wani farfesa ne a sashen nazari game da kwari. Sa’ad da yake kwaleji, an koya masa juyin halitta. Ya ce: “A duk lokacin da muka yi jarrabawa, nakan ba wa malamaina amsar da suke so amma ban gaskata abin da suka koya mini ba.”

Amma me ya sa yake ma wasu mutane wuya su amince da koyarwar juyin halitta, har da ’yan kimiyya? Don mu fahimci dalilin, bari mu bincika wasu tambayoyi biyu da masu bincike suke fama da su: (1) Ta yaya rayuwa ta soma? da kuma (2) Daga ina ne abubuwa masu rai suka fito?

Ta Yaya Rayuwa Ta Soma?

ABIN DA WASU SUKA CE. Rayuwa ta soma ne daga abubuwa marasa rai.

ME YA SA WASU BA SU GAMSU DA WANNAN AMSAR BA? Domin duk da cewa ’yan kimiyya sun dada fahimtar yadda aka tsara kwayoyin halittar rai yanzu fiye da dā, har ila ba su iya bayyana da kyau ko mene ne rai ba. Kari ga haka akwai bambanci sosai tsakanin kwayar halittar rai mafi sauki da abubuwa marasa rai.

’Yan kimiyya ba su san ainihin yadda duniya take biliyoyin shekaru da suka shige ba, abin da suke tsammani ne kawai suke fada. Ban da haka ma, ra’ayinsu game da yadda rai ya soma ya bambanta. Alal misali, wasu sun ce rai ya soma ne cikin dutse mai aman wuta ko kuma daga karkashin teku. Wasu kuma sun gaskata cewa abubuwan da suka hadu suka zama rai sun soma ne a wani wuri a sararin samaniya, sai daga baya suka fado duniya cikin duwatsun da ke fadowa daga sarari. Amma hakan bai bayyana yadda rai ya soma ba. Akasin haka, ya dai nuna cewa rai ya soma ne a wani wuri.

Kari ga haka, ’yan kimiyya sun ce wasu kananan sinadarai da suka wanzu tun dā ne suka zama kwayoyin da ke dauke da bayanai game da dan Adam. Sun ce sinadaran nan sun fito ne haka kawai daga abubuwa marasa rai da ba sa saurin canjawa kuma suna iya haifar da wasu makamantansu. Amma ’yan kimiyya ba su da wani tabbaci cewa irin wadannan sinadaran sun taba wanzuwa, kuma sun kasa kera irin su a dakin gwaje-gwaje.

Abubuwa masu rai sun fita dabam daga sauran halittu a yadda suke ajiyar bayanai da kuma amfani da su. Kwayoyin halittar rai suna daukan bayanan da ke nuna yadda ya kamata kowannensu ya zama, sukan fassara bayanan kuma su yi amfani da su. Wasu ’yan kimiyya sun kwatanta bayanai game da dan Adam da bayanan da ke cikin kwamfuta kuma sun ce abubuwan da ke dauke da wadannan bayanan na kamar kwamfutar da kanta. Amma koyarwar juyin halitta ta kasa nuna ko daga ina ne wadannan bayanan suka fito.

Kwayar halittar rai ba za ta iya yin aiki ba tare da sinadaran furotin ba. Kuma sinadarin furotin daya yana dauke da darurruwan kwayoyin da ake kira amino acid da aka harhada su a hanya ta musamman. Ban da haka, dole ne wadannan sinadaran furotin su nannadu kuma su dauki wata siffa ta musamman kafin su kasance da amfani. Wasu ’yan kimiyya sun ce zai yi wuya sosai a ce sinadarin furotin kwaya daya ya fito da kansa. Wani dan kimiyya mai suna Paul Davies ya ce, “Tun da yake kwayar halittar rai daya tana bukatar dubban sinadaran furotin dabam-dabam kafin ta yi aiki, ba zai yiwu a ce wadannan kwayoyin halitta sun fito da kansu ba.”

GASKIYAR BATUN. Bayan an yi shekaru da dama ana bincike a kusan dukan fannonin kimiyya, an gano cewa abubuwa masu rai ne suke haifar da abubuwa masu rai, kamar yadda muka sani.

Daga Ina Ne Abubuwa Masu Rai Suka Fito?

ABIN DA WASU SUKA CE. Abu mai rai na farko ne ya yi girma a hankali, kuma da kansa ya yi ta canjawa har ya zama wasu abubuwa masu rai, har da ’yan Adam.

ME YA SA WASU BA SU GAMSU DA WANNAN AMSAR BA? Wasu kwayoyin halittar rai sun fi wasu a fannoni da dama. Wani littafin bincike ya ce koyarwar nan cewa karamar kwayar halittar rai za ta iya canjawa ta zama babba, ita ce “koyarwa ta biyu a karkashin koyarwar juyin halitta da ba za a iya ganewa ba bayan abin da aka fada game da yadda rayuwa ta soma.”

’Yan kimiyya sun gano cewa kowace kwayar halittar rai tana dauke da sinadaran furotin da suke aiki tare wajen yin ayyuka masu wuya. Wadannan ayyukan sun kunshi daukan abinci zuwa gabobin jiki dabam-dabam da sarrafa su don ba da kuzari da gyara kwayoyin halitta da aika sakonni. Zai yiwu a ce wani abu mai rai ne ya yi ta canjawa kuma ya tsara kansa haka kawai har ya fid da irin wadannan kwayoyin halitta masu ban al’ajabi? Mutane da dama suna ganin hakan ba zai yiwu ba.

Kwai guda ne yake girma ya zama mutum ko kuma dabba. Yayin da kwan yake girma, kwayoyin halitta da ke cikinsa sukan haifar da wasu kwayoyi. Yayin da kwayoyin suke karuwa, sukan kasu kuma su dauki kamanni dabam-dabam domin su gina gabobin jiki dabam-dabam. Hakika, koyarwar juyin halitta ba za ta iya bayyana yadda kowace kwayar halitta ke “sanin” abin da zai zama da kuma inda zai kasance a cikin jiki ba.

’Yan kimiyya sun gano cewa kafin wata dabba ta iya canjawa ta zama wata irin dabba dabam, dole ne canjin ya soma daga cikin kwayoyin halittar wannan dabbar. Tun da ’yan kimiyya da kansu ba su iya nuna yadda juyin halitta ta iya fid da kwayar halitta “mafi kankanta” ba, zai yiwu a ce wani abu mai rai ne ya yi ta canjawa da kansa, har ya fid da dukan ire-iren dabobbin da muke da su a yau? Wani farfesa a fannin kimiyyar abubuwa masu rai mai suna Michael Behe ya yi magana game da tsarin jikunan dabbobi. Ya ce ko da yake ’yan Adam “sun fahimci yadda aka tsara jikunan dabobbi sosai yanzu kuma mun gano abubuwa masu wuya da kuma ban al’ajabi game da su, har yanzu ba a sami kwakkwaran dalilin da ya nuna cewa wannan tsari mai wuya zai fito haka kawai ba tare da wani ya yi su ba.”

’Yan Adam suna iya sanin abubuwan da ke faruwa kewaye da su, suna iya yin tunani da kuma bincike. Ban da haka ma, suna iya zama da halaye masu kyau kamar karimci da sadaukarwa kuma suna iya bambanta abin da ya dace da wanda bai dace ba. Koyarwar juyin halitta ba za ta iya bayyana yadda mutane suke iya kasancewa da wadannan halayen ba.

GASKIYAR BATUN. Ko da yake mutane da dama sun nace cewa koyarwar juyin halitta gaskiya ce, wasu ba su gamsu da abin da koyarwar juyin halitta ta fada game da yadda rai ya soma da kuma yadda ya fid da sauran halittu ba.

Amsar da Ta Cancanci Mu Bincika

Abubuwan da mutane da dama suke gani ne ya sa sun kammala cewa wani da ya fi ’yan Adam hikima ne ya halicci dukan abubuwa masu rai. Ka yi la’akari da misalin Antony Flew wani farfesa na ilimin falsafa. A dā bai yarda cewa akwai Allah ba kuma yana cikin wadanda suke yada wannan ra’ayin sosai. Amma da ya koyi game da tsari mai ban mamaki da halittu suke da shi, da kuma ka’idodin da ke ja-gorar dukan halittun da ke sararin samaniya, sai ya canja ra’ayinsa. Da yake kaulin ra’ayin masu ilimin falsafa da suka riga shi, Flew ya ce: “Dole ne mu amince da abin da bincike ya nuna.” A gare shi, sakamakon binciken da aka yi ya nuna cewa akwai Mahalicci.

Gerard ma, wanda aka ambata a farkon wannan talifin ya yarda da hakan. Duk da cewa ya yi karatu sosai kuma ya kware wajen nazari game da kwari, ya ce: “Ban ga wani tabbaci da ya nuna cewa rai ya fito ne haka kawai daga abubuwa marasa rai ba. Yadda aka tsara halittu masu rai da yadda suke yin abubuwa da dama masu wuya, ya tabbatar mini cewa akwai Wanda ya tsara da kuma siffanta su.”

Kallon zanen da wani mai zane ya yi zai iya sa ka san halinsa, hakazalika yin bincike game da halittu ya taimaka wa Gerard ya fahimci halayen Mahaliccinsu. Gerard ya kuma dauki lokaci yana nazarin littafin da Mahaliccinmu ya wallafa, wato Littafi Mai Tsarki. (2 Timoti 3:​16) A cikinsa ya sami amsoshi masu gamsarwa game da tarihin ’yan Adam da kuma yadda za a iya shawo kan matsalolin da mutane suke fama da su a yau. Hakan ya tabbatar masa cewa wani mai hikima fiye da ’yan Adam ne ya wallafa Littafi Mai Tsarki.

Kamar Gerard, kai ma za ka amfana idan ka bincika abin da Littafi Mai Tsarki ya fada game da yadda rayuwa ta soma. Za mu so ka bincika littafin don ka tabbatar wa kanka.