Koma ka ga abin da ke ciki

HALITTARSA AKA YI?

Kafaffun Masu Ban Mamaki na Kifin Octopus

Kafaffun Masu Ban Mamaki na Kifin Octopus

 Injiniyoyi suna kokarin kera wata na’ura da za ta taimaka wa likitoci su yi tiyata mai wuya a hanya mai sauki. Yadda kifin Octopus yake yin abubuwa dabam-dabam da kafaffunsa ne ya sa injiniyoyi suke so su yi kwaikwayonsa.

 Alal misali: Kifin Octopus yana iya kama da rike da kuma murde abubuwa da kafaffunsa guda takwas ko a wurin da bai da fadi sosai. Kari ga haka, kifin yana iya lankwashe kafaffunsa na kowane bangare kuma ya sa wasu sashen kafaffunsa ya kangare idan bukata ta kama.

 Masu bincike sun gaskata cewa kera na’ura da ke da hannu mai laushi da za a iya jujjuyawa zai taimaka wa likitocin yin tiyata ba tare da yanka jikin majiyyata sosai ba. Irin wannan na’urar za ta taimaka a bi tsarin yin tiyata mai sauki.

 Ka duba yadda kifin Octopus yake amfani da kafaffunsa a hanyoyi dabam-dabam

 An riga an kera irin wannan na’ura mai hannu da za a iya jujjuyawa don yin tiyata. Wani sashe a na’urar mai inci 5 zai iya daga da kuma rike wasu gabobi a jiki ba tare da jawo wata illa ba, wani sashe kuma zai iya yin ainihin tiyatar. Wani likita mai suna Tommaso Ranzani da ke cikin rukunin da suka kera na’urar ya ce: “Mun gaskata cewa wannan soma tabi ne kuma za a ci gaba da kyautata wannan na’urar.”

Na’ura da ke da hannu mai laushi da za a iya jujjuyawa za ta taimaka wa likitoci yin tiyata

 Mene ne ra’ayinka? Kana ganin cewa yadda kifin Octopus yake jujjuya kafaffunsa sakamakon juyin halitta ne? Ko akwai wanda ya halicce shi?