Koma ka ga abin da ke ciki

HALITTARSA AKA YI?

Farin Malam-Bude-Littafi

Farin Malam-Bude-Littafi

Malam-bude-littafi yana dogara ga zafin rana don ya sami karfin tashi. Amma a lokacin da akwai hazo, farin malam-bude-littafi yana iya tashiwa kafin sauran malam-bude-littafi su iya tashi. Ta yaya yake yin hakan?

Ka yi la’akari da wannan: Kafin ya sami isashen zafin rana, malam-bude-littafi yana zama a cikin rana da fikafikansu a rufe. Amma farin malam-bude-littafi yana barin nasa fikafikai a bude. Masana sun gano cewa kafin malam-bude-littafi ya sami isashen zafin rana, yana bukatar ya dan daga fikafikansa sama. Yin hakan yana sa ya sami zafin rana kai tsaye a jijiyoyi da suke taimaka masa ya tashi.

Masu bincike a makarantar jami’ar Exeter da ke Ingila sun yi bincike don sanin ko za a iya inganta na’urar wutar lantarki da ke amfani da hasken rana. Suna son yin hakan ta wajen kwaikwayon yadda fikafikan farin malam-bude-littafi yake. Ta yin hakan, sun gano cewa karfin wutar lantarkin da aka samo ya karu da kusan kashi 50 cikin dari.

A binciken, sun sake gano cewa fikafikan farin malam-bude-littafi yana kamar madubi. Ta wajen yin kwaikwayon yadda fikafikan suke, da kuma yadda suke kama da madubi, masu bincike sun kera na’urar wutar lantarki da ke amfani da hasken rana da bai da nauyi sosai kuma yake da inganci. Sakamakon da aka samu ya sa wani farfesa mai suna Richard ffrench-Constant ya ba farin malam-bude-littafi suna, ya kira shi “gwani a yin amfani da hasken rana yadda ya dace.”

Mene ne ra’ayinka? Kana ganin cewa Farin Malam-bude-littafi sakamakon juyin halitta ne? Ko akwai wanda ya halicce shi?