Koma ka ga abin da ke ciki

HALITTARSA AKA YI?

An Halicci Fatar Wata irin Tsutsar Ruwa a Hanya Mai Ban Mamaki

An Halicci Fatar Wata irin Tsutsar Ruwa a Hanya Mai Ban Mamaki

Irin wannan tsutsar suna zama ne a karkashin teku. Fatar tsutsar tana da gudaje. Suna iya bi da jikinsu yadda suke so, suna iya sa fatarsu ta yi laushi ko kuma ta yi tauri sosai a cikin ’yan mintoci. Yin hakan yana taimaka musu su iya shiga matsatsen wuri kuma su sa fatarsu ta yi tauri don kada wani abu ya cutar da su. Fatarsu ce ke taimaka wa irin wannan tsutsar su yi wadannan abubuwan.

Ka yi la’akari da wannan: Tsutsar tana iya sa fatarta ta yi laushi ko tauri ko kuma ta bar shi daidai yanayin jikinta. Don cim ma hakan, wannan tsutsar tana amfani da jijiyoyi a jikinta da suke taimaka mata. Jijiyoyin suna taimaka mata ta wajen yin amfani da sinadarai dabam-dabam da ke sa abu tauri ko laushi.

Idan tana so fatarta ta yi tauri tana sake sinadarin da ke sa jijiyoyin fatarta su yi tauri sosai. Sa’ad da take so fatar ta yi laushi, tana sake sinadarin da ke sa jijiyoyin fatar yin laushi. Fatar tana yin laushi sosai kamar za ta narke.

Masana kimiyya suna kwaikwayon yadda fatar wannan tsutsar take domin kera abubuwan da za su iya canjawa a yanayi dabam-dabam. Daya daga cikin abubuwan da suke so su kera a irin wannan hanyar ita ce electrodes wato abin da ake amfani da shi don yin tiyata a kwakwalwa. Kuma sa’ad da aka saka abin a daidai wurin da ake so a yi tiyatar sai ya yi laushi ba tare da bata lokaci ba. Idan aka cim ma haka, watakila ba za a rika samun matsaloli sa’ad da ake tiyata a kwakwalwa ba.

Mene ne ra’ayinka? Kana ganin cewa yadda fatar wannan tsutsar ruwa take sakamakon juyin halitta ne? Ko akwai wanda ya halicce ta?