Koma ka ga abin da ke ciki

Halittarsa Aka Yi?

Dabbobin da ke Doron Duniya

Harshen Kule​—Halittarsa Aka Yi?

Idan ba barci kuliyoyi suke yi ba, za su iya daukan wajen awa daya cikin awa hudu suna tsabtace gashinsu. Me yake taimaka musu su tsabtace kansu da kyau?

Karfin Sansanawa na Kare

Mene ne masanan kimiyya suka gani a yadda kare yake sansanawa da suke so su kwaikwayi?

Dabbar Slug na da Gansakuka Mai Kama da Gam

Ya kamata kowane likita mai yin tiyata ya kasance da gam da ke kamar gamsakuka na dabbar slug a cikin kayan aikinsa. Hakan zai sa a daina dinka jikin mutum sa’ad da aka yi masa tiyata ko kuma yin amfani da wayoyi sa’ad da aka yi tiyata.

Halittun Ruwa

Fatar Kifin Shark​—Halittarsa Aka Yi?

A wace hanya ce tsarin fatar kifin shark yake hana kwayoyin cuta zama a kansa?

Wata Babban Dabbar Ruwa Mai Fata da ke Tsabtace Kanta

Me ya sa kamfanoni masu tura abubuwa zuwa wurare dabam-dabam suke son sanin yadda dabbar nan ke tsabtacce kanta?

Yadda Dolfin Ke Sanin Zurfin Ruwa

Masu bincike sun duba abin da ke sa dabbar dolfin yin kara da jin abubuwa kuma suka yi kokarin kwaikwayon sa.

Abu Mai Yauki da Ke Jikin Kifin da Ake Kira Hagfish​—Halittarsa Aka Yi?

Halittu da suke so su cinye kifin sun tsane shi, amma yana burge ’yan kimiyya. Me ya sa?

An Halicci Fatar Wata irin Tsutsar Ruwa a Hanya Mai Ban Mamaki

Mene ne yake taimaka wa fatar wannan tsutsar ruwa ta rika canja a yanayi dabam-dabam?

Yadda Aka Tsara Hakoran Wani Irin Dodon Kodi Mai Suna Limpet

Mene ne ya sa hakoran dodon kodi mai suna limpet suka fi sakar gizo-gizo karfi?

Gam Din Wani Abu Mai Kama da Dodon Kodi

Gam din abu mai rai da ke kama da dodon kodi ya fi duk abin da ke manne wa abubuwa. Bai dade ba da masana suka gano yadda abubuwa masu rai da ke kama da dodon kodi suke manne wa wuraren da ke jike.

Kafaffun Masu Ban Mamaki na Kifin Octopus

Injiniyoyi sun kera na’ura mai hannu da zai iya yin abu mai ban al’ajabi.

Wutsiyar Dokin Ruwa

Dokin ruwa kifi ne mai wutsiya da aka tsara a hanya mai al’ajabi da ake son a yi kwaikwayonsa don a kera na’urori dabam-dabam.

Abin da Kifin Remora Yake Makalewa a Jikin Dabbobi da Shi​—Halittarsa Aka Yi?

Me yake taimaka ma wannan kifin ya iya mannewa gam-gam a jikin wasu dabbobi?

Tsuntsaye

Tsuntsayen gannet suna shiga ruwa​​—⁠Halittarsa Aka Yi?

Me ya wadannan tsuntsayen ba sa jin rauni bayan sun shiga ruwa da karfin da ya wuce na maganadiso sau 20?

Kalar Tsuntsu da Ba Ya Taba Kodewa

Ta yaya kalar fukafukan tsuntsu da ba ya kodewa za su taimaka wajen yin fenti da yadi masu kyau?

Fikafikin Mujiya

Kwaikwayon yadda aka tsara fikafikin mujiya zai taimaka a kera farfelar injin turbin da zai rage yin kara.

Kwari

Abin da Ya Sa Kudan Zuma da Ake Kira Bumblebee Ke Firiya Sosai​—Halittarsa Aka Yi?

Ta yaya wannan karamar kudan zuma ke iya firiya sosai fiye da kwararrun matukan jirgin sama?

Me Ya Sa Tururuwa Ba Sa Go-sulo?

Tururuwa ba sa cunkosuwa ko kadan. Yaya suke yin hakan?

Tururuwa Mai Wanka

Wannan karamar tururuwar tana bukatar ta tsabtace kanta don kada ta mutu. Ta yaya take yin wannan aikin?

Farin Malam-Bude-Littafi

Mene ne injiniyoyi suka gani a jikin farin malam-bude-littafi da ya taimaka musu su yi gyara ga na’urar wutar lantarki da ke amfani da hasken rana da suke kerawa?

Yadda Kuda Yake Tashi da Kuma Juyawa

Wadannan kwarin suna juya kamar jiragen yaki sau da yawa a cikin sakan daya.

Shuke-Shuke

Abin da Ya Sa Lemun Pomelo Ba Ya Fashewa​—⁠Halittarsa Aka Yi?

Ta yaya masana kimiyya suke so su yi amfani da fasalin lemun pomelo?